Antin Yara 11 - 20 Hausa Novel Complete.
Azumi yanata tafiya,abdallah se samun kayan sallah yakeyi agun jama'a. Dan shine mai kiran sallah a masallaci gashi da shiga rai. Ranan manosh manosh da marwan sunje girei se marwan yace aboki abdallah zoka gaisa da abokina wanda zai auri auntyn yara.
Abdallah yazo suka gaisa cikin fara'a yace dama kaine kake neman auntynah,manosh yace eh nine,abdallah yace to Allah ka rik'eta da amana karka cutar da ita dan Allah dan ance soja suna dukan matansu. Dariya sosai su manosh sukayi sannanya rik'o hannun abdallah yace har abada abdallah,karka sa ranni zan wulak'anta maryam domin ina k'aunarta fiye da yadda nake k'aunar kaika kuma wlh bacika baki nake makaba kaji? Abdallah yace alhamdulillah naji dad'i sosai Allah ya tabbatar muku da alkhairi,sukace ameen,sannan yace auntyn yara ta aikeni bari aje aje na dawo,sukace to seka dawo sannan ya tafi.
Abdallah yaje gunda uncle ibrahim yake da friends nashi yamusu slm tare da gaisuwa sannan yace yah ibrahim gurinka nazo an aikoni,ibrahim yace to ina jinka,se kuma abdallan yayi shuru,ganin shurunne ibrahim ya mik'e yace to muje gefe ka kaya mun.
Bayan sun koma gefene abdallah yace yah ibrahim auntyn yara ce ta aikoni gunka,dad'i sosai ibrahim yaji da akace auntyn yara yana sonji menene aikan. Abdallah yace tace wai tayita kiran number'nka amma yak'i tafiya,wai inzo ince maka tayi bak'i kuma tana so gu gaisa dasu. Ibrahim yace bak'i wani iri maza ko mata?abdallah yace maza wanda yake nemanta da kuma aunty rashida. K'irjin ibrahim ya buga sosai yace abdallah dama zance danaji da gaskene kenan akan auntyn yara?
abdulmkibab. hexat. com Abdallah yace eh yaya hakane tare da sunkuyar da kansa k'asa yana tusayin yayan nashi don shi kad'ai yasan irin k'aunar auntyn yara da yakeyi amma dayake bai gama karatunshiba shiyasama baiyiwa mahaifinta magana akaiba yafiso seya gama komai na karatunshi. Ibrahim yace kaje ina zuwa,sannan abdallah ya tafi jikinshi a sanyaye.
Ibrahim ya kunna wayanshi ya kira number'n maryam ringing d'aya ta d'aunka tare da salma,wani irin dad'i yaji har cikin ranshi dajin daddad'ar muryanta. Yace aunty wai kina nemana,murmushi tayi tace eh na kira wayanka ban samuba,yace wlh na kashene saka makon damuna da akayi,tace eyyah,yace ganinan ina zuwa ki basu hakuri kinji,tace laa bakomai wlh sunanan a waje dama gurinka kawai sukazo. Yace tonagode da mutuntani da kikayi aunty se anjuma,tace bakomai aikafi haka a guna uncle ibrahima nima nagode.
Koda ya ajiye wayan shi kad'ai yasan meyakeji a cikin ranshi game da maryam.
Ya k'arasa gumsu da sallama suka gaisa sosai kuma cikin fara'a dama shi ibrahim na kowane kamar dai maryam d'in. Hira sukayi sosai kamar sun dad'e da sanin juna,yayi musu tambayoyi suka bashi amsan gaskya domin wani abunba manosh b'oyewa yakeyi,sam bayaso asan mahaifinshi mai arzikine. Haka sukaitayidai har suka gama sannan suka sallama ibrahim ya wuce gida,se manosh ya kira maryam a waya yace aunt pls ki fito in ganki zamu wuce,tace har gun gaisa kenan zaku tafi,yace eh wlh ibrahim yana da kirki sosai wlh gaskya naji dad'in had'uwa dashi,dad'i taji da aka yabi ibrahim tace nagode nidai bazan fitoba aiba gurina kazoba,ya marairaice murya yace pls aunt kinga marwan yanata min dariya ai gara shi tunda rashi bata nan hankalinsa a kwance "pls come aou aunt"kodon fita kunya a idon marwan don wlh yau idan muka koma shimenan ya samu abun tsokana harsu majid sesunji.
Dariya tayi tare da katse wayar d'inkin atamface a jikinta na fitet gaun seta sa himar iya gwinwanta ta fito.
Tunda ya hangota yake murmushi tare da k'are mata kallo harta iso gunsu tana murmushi,marwan yace ai wlh banso ki fito har addu'a nakeyi a raina amma se gashi kin fito meyasa aunt,mirmushi tayi tace saboda banaso ku mishi dariya,manosh yace "thankyou aunt"tare da kaiwa marwan bugu a bayansa yayi saurin shigewa mota gurin tuk'i ya rufe kofar maryam tanata dariya. Manosh ya dawo da kallonshi kan maryam yace wato har kin fara min yanga ko,tace aiba yana bane dama gun uncle ibrahim kukazo ba gunmuba,yace eh amma dai ai kinsan zanso in gaki ko,tace to ai gashi ka ganni kuma ni zan wuce gida,yace nidai ban sallamekiba tukunna,tace to sallameni,murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau tana kallonshi shi kuwa wani gurin yake kallo daban.
Tace wlh ka dingayin mirmushi yana k'ara maka kyau,dad'i yaji sosai yace wauace ki kalleni,mirmushi tayi tace ni ban kallekaba kawai dai na fad'a makane,yace kin kalleni mana kuma ai ke kika sani na fara murmushi sosai wlh,tace ahakan,yace "yes" ki tambayi miher zata gaya miki ni gaskya bancikayin fara'aba, yace hmmm to gaskya nidai ka dinga yi kaji,yace ai inayi kuma danke.
Tace to shikenan zan wuce,yace meyasa kikemin hakane aunt kodon kinga ina sonki sosaine shiyasa kike min haka,tace a'a wlh aiba guna kazoba kuma ai min gaisa,yace to shikenan mun tafi,tace kayi fushi kenan,yace a'a banyiba kawai dai zamu tafine,kallonshi takeyi amma sam yak'i kallonta kuma yana tsaye yana fiskantarta,tace toshikenan Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan ta juya ta shiga gida,mota ya bud'e yashiga marwan yaja suka tafi.
Manosh ya saba idan suka bar girei seya kira maryam a hanya,amma yau sam sebai kirataba abun yad'an dameta tace to kodai fushi yayine? Har bayan 2hrs bai kiraba,kuma a wannan lokacin tasan suna gida,marwan ne ya kirata yace aunt mun iso gida lfy,tace alhamdulillah tona gode sosai,yace bakomai wlh mune da godiya sannan sukayi sallama.
Har bayan isha manosh bai kira maryam se taji taba kyauta mishiba dan tasan fushi yayi dukda dai basu tab'a samun matsalaba se yau. Har 9:00pm seta d'auki wayanta ta kirashi yanata ringing harya d'auke,zata sake kira kenan setaga call d'inshi,ta d'auka cikin sanyin murya tace hello
Shuru yayi baice komaiba ta sake cewa hello.
Nanma shuru yak'i yayi magana, tace hello manosh.
Karon farko data kira sunanshi kenan,seyaji dad'i har cikin ranshi amma baice komaiba,ta sake cewa "manosh pls talk 2me" yace me kike so nace miki aunt? Tace wai fushi kakeyi danine, shuru yayi uanajin daddad'ar muryanta,ta sake cewa "manosh am talking to you" yace inace ni kike kora agaban marwan ko? Wani iri taji a ranta dan yadda yayi maganan batasan lokacin datace "am so sorry manosh i din't main to hurt you pls?".
Nanma shuru yayi,ta sake cewa manosh wai bazaka min magana bane kuma kanajina? Yace "yes" take jikinta yayi sanyi tace manosh am sorry pls,nanma shuru yayi seta katse wayan.
Hankalinta ya tashi sosai tayi dana sanin yimasa hakan.
Har 10pm manosh bai sake kirantaba,seta tsinci kanta cikin damuwa sosai sam ta kasa sakewa,dan tana son manosh sosai acikin ranta. K'arar shigowar texs tayi a wayanta da sauri ta d'auka ta bud'e taga
Am sorry too apple
I love you so much
Nd i will call you leta.
Am talking with my dad now okey,manosh loves you so verry much apple.
Maryam tana gama karanta texs d'in taji dad'i sosai a ranta tayi murmushi tana mai k'ara jin sonshi na ratsa jikinta,tace i love you too peach tare da rufe idanunta tana murmushi..
1 Comments
Baccarat | Learn how to play the game of Baccarat and win
ReplyDeleteLearn all you need to know about 토토사이트 the Baccarat table game in Baccarat. This game febcasino has a lot to offer. 실시간 카지노 사이트 Learn how to 파라오 카지노 play the 63카지노 game in this online casino and the rules.